Hukumar Alhazai ta Najeriya ta fitar da jadawalin aikin Hajjin shekarar 2026, wanda ya kunshi sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da mahukuntan Saudiyya a watan Nuwamba na shekarar 2025, da kammala biyan kudade a sansanonin zuwa ranar 4 ga watan Janairu, da kulla kwangilolin sufuri da masauki zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu, da tabbatar da bayar da biza zuwa watan Maris 2026.
Hukumar ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar da bin wadannan tsare-tsare domin tabbatar da aikin ga alhazan Najeriya lami lafiya
