Gwamnatin Najeriya ta kammala yin nazari sosai kan tsarin karatu na kasa, na makarantun firamare da sakandare, da na koyon fasaha.

Sabon tsarin yana da nufin rage yawan ababen dake kunshe a ciki, inganta sakamakon koyo, da kuma baiwa ɗalibai ƙwarewa daidai da matakin duniya.

An gudanar da bitar ne tare da hadin gwiwar wasu manyan hukumomi da suka hada da Hukumar Bincike da Cigaban Ilimi ta Najeriya, da Hukumar Ilimi ta bai daya, da Hukumar Kula da Manyan Sakandare ta Kasa, da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *