Najeriya na fuskantar nau’i uku na rashin abinci mai gina jiki, wanda kuma aka fi sani da “yunwar boye.”
Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a samar da ingantaccen tsari don magance wannan matsala, tare da yin kira ga tsauraran dokoki, tallafawa samar da kayayyaki na gida, da kuma amfani da fasaha kamar dandamalin Digital Forification Quality Traceability Plus.
Ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta kuma jaddada mahimmancin kayyade abinci wajen inganta lafiyar jama’a, rage farashin kiwon lafiya, da kuma bunkasa yawan
aiki.
An yi kira ga gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin jama’a, da abokan ci gaba da su saka hannun jari a samar da kayayyaki a cikin gida tare da yin amfani da fasaha don sa ido kan bin ka’idodin.
Binciken Kiwon Lafiyar Jama’a na Najeriya na 2024 ya nuna cewa kashi 40% na yara masu shekaru 6 zuwa 59 na fama da karancin abinci, kuma kashi 79% na ‘yan Najeriya na fama da karancin abinci.
