Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tashar jiragen ruwa ta Baro ya gano rashin hadin kai a tsakanin hukumomin gwamnati da kuma nakasu na ababen more rayuwa a matsayin babban koma baya da ya shafi ayyukan ta. Kwamitin yana neman haɗin gwiwa tare da Media Trust Group don ƙaddamar da shawarwari da haɗin gwiwar jama’a.
