Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a gabar tekun Mauritaniya, inda mutane 69 suka mutu. Kwale-kwalen ya kife ne lokacin da bakin haure suka ga hasken wani gari sa’annan suka koma gefe guda. Wani babban jami’in tsaron gabar teku ya tabbatar da cewa an ceto mutane 17. Kwale-kwalen ya bar Gambiya mako guda kafin nan tare da mutane kusan 160. Kifewar kwale-kwale ya zama ruwan dare yayin yunkurin ketare tsakanin Afirka da Turai, tare da magudanar ruwa mai ƙarfi da tasoshin da ke sa tafiyar ta kasance mai haɗari.
Migrants aboard a Guradia di Finanza and Navy military vessel are tranferred from the so-called migrant "Hotspot" operational processing facility on the southern Italian Island of Lampedusa, south of Sicily, to another center, on July 11, 2022. (Photo by Alessandro SERRANO / AFP) 